Ƴan Najeriya a duk jihohin Najeriya sun yarda da Peter Obi da LP — Ozigbo
Shahararren dan kasuwa Valentine Ozigbo ya ce Peter Obi da Labour Party (LP) sun samu karbuwa a duk jihohin Najeriya.
Ozigbo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a bikin cika shekaru 31 da kafuwar Anambra.
Ya kuma ja hankalin al’ummar jihar da su bayar da nasu gudunmuwar wajen ganin an ciyar da siyasa a kasar nan a gaba.
KARANTA WANNAN LABARIN:
Dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP a 2021 ya bayyana fatan cewa zaben 2023 zai haifar da juyin juya hali na cigaba a fagen siyasar Anambra.
Da yake lura da cewa jihar ta samu “ci gaba maras kyau”, Ozigbo ya bukaci ‘yan kasar da su ba da fifiko da cancantar shugabanni da hanyoyin da suke bi su zamanto Shuwagabannin.
Ya yi imanin cewa Anambra ba ta shan wahala saboda ƙarancin ƙwararrun mutane a siyasa amma saboda jagorancin jam’iyyu da tsare-tsare suna lalata ko hana waɗanda za su iya samun canji mai kyau.
‘Yayin da za mu nemi shugabanci nagari, Ndi Anambra za su iya bugun kirji su ce an yi musu abun kirki idan aka kwatanta da sauran jihohi.
“Mun samu shugabanni da dama da suka bar aikinsu kuma suka taka rawar gani wajen samar da jihar.
“Abin farin ciki, daya daga cikin shugabannin da suka fi tasiri a tarihin mu (Obi) yana yunƙurin zama shugaban Najeriya tare da yin koyi da irin shugabanci na musamman da ya sa ya samu yabo a duniya.”
Ya kara da cewa 2023 na nuni da cewa dole ne ‘yan Najeriya su samu daidaito a kowane mataki.
A ranar Talatar da ta gabata ne Obi da shugabannin jam’iyyar na kasa suka karbe Ozigbo da kungiyarsa ta siyasa ta Anambra Chawapu.
A wani Labarin kuma:Zazzaɓin Lassa Ya Kama Mutane 894 a Najeriya – NCDC
Adadin waɗanda suka kamu da zazzabin Lassa tun daga farkon Shekarar 2022 ya kai 894, yayin da mutane 168 suka mutu, a cewar Cibiyar Kula da Manyan Cututtuka ta Najeriya.
Rahoton na baya-bayan nan da Hukumar NCDC ta fitar na mako na 33 ya kuma nuna cewa akwai mutane 6392 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗin Ƙananan Hukumomi 101 da ke a cikin Jihohi 25.