Gwamnan Taraba Ishaku Darius, “yace kamata yayi bautar kasa ya koma shekara biyu, domin Dalibai su runka samun horon sojoji.”
Ya bayyana hakane lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channel Tv, yace “hakan zai basu damar samun yadda za su kare kansu.” Kamar yadda Jaridar Cable ta wallafa
Yace tunda yanzu gwamnati ta Kasa samar da ingantaccen tsaro mutane su fara kare kansu.
KARANTABABBAR MAGANA: An garkame masu gadi kan laifin satar kayan ma’aikata
Yace “Idan za’a bi ta tawa, dole bautar kasa ya koma shekara biyu shekarar farko zama gidan soja don samun horo, dayar shekarar kuma su cigaba da ayyukan su.”
“Hakan zai baiwa matasa damar daukar bindiga don kare kansu, kamar yadda akeyi a Isiraila da kuma Lebanon.”
“Ya kamata gwamnati ta koyawa Yan kasa dabarun kare Kai tunda ta Kasa samar da tsaro.”
Ya kumayi kira ga gwamnati da ta baiwa wadanda ke zama a kan iyaka horo kan yadda za su kare kansu daga Yan bindiga da masu garkuwa da mutane.”
Yace irin wannan gurare bai kamata a bar su hakanan ba sai abunda Yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka gadamar yi a garinsu.
“Har yanzu ina rokon gwamnatin tarayya da ta baiwa mazauna kauyukan da shigar su keda wuya damar daukan makamai don kare kansu.”