A ranar Laraba ne Hukumar EFCC tacewa babban Kotu Najeriya dake Abuja Abubakar Bukola Saraki na kokarin hana mu tabbatar da laifinsa.
Jagoran hukumar ta EFCC kan binciken Saraki, Chile Okoronkwo ya bayyanawa mai Shari’a Awunli Chikere lokacin da kungiyar kare hakkin Dan adam ta gabatar da tsohon shugaban Yan majalisu Abubakar Bukola Saraki a Kotu. Kamar yadda Jaridar The news Nigeria ta wallafa a shafinta
Hukumar ta EFCC a shekarar 2019 tace, za ta gabatar da abunda Abubakar Bukola Saraki yake samu tun daga 2003 har zuwa 2011 lokacin yana gwamnan Jahar Kwara.
KARANTA:- Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashin kara himma wajan tabbatar da lafiya a Jahar Sokoto
Hukumar ta ruwaito cewar an kwace wasu gidajen shi dake Ikonyi a Jahar Legas a lokacin.
Hukumar yada labarai ta Najeriya ta ruwaito cewar, a ranar goma ga watan May shekarar 2019 an gabatar da karar Abubakar Bukola Saraki a gaban Kotu da takadda mai lamba FHC/ABJ/CS/507/19 da FHC/ABJ/CS/508/19 gaban mai Shari’a Taiwo Taiwo inda yake tuhumar hukumar ta EFCC.
Alkali Taiwo mai Jagorantar shari’ar ya cigaba da sauran karar da hukumar ta EFCC ta gabatar tare da sauran masu kare su guda biyar, inda yace musu su cigaba da binciko hujjoji akan karar, sannan aka dage shari’ar zuwa wani lokacin.
An baiwa Abubakar Bukola Saraki dama ne bayan mai kareshi ya gabatar da wata takarda a ranar 14 ga watan May a shekarar 2019.
Wadanda suke cikin shari’ar sun hada da Attorney General of the Federation (AGF), Inspector-General of Police (IGP), State Security Service (SSS), Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) and Code of Conduct Bureau (CCB) da masu kare shari’ar na 1st, 2nd, 3rd, 5th sannan da 6th.
Kotun dai ta sanar da mai kara da wanda ake kara dasu bar shari’ar.
Sai dai Alkalin hukumar ta EFCC yace da akwai takarda da zai gabatarwa kotu.
Alkalin ya cigaba da cewa, a kwai wata kotu wadda Taiwo ya Jagoranta tace masu kara su cigaba da nemo hujjoji akan karar.
Sai dai hakan ya jawo hana masu karar guda hudu kaddamar da aikinsu har na tsawon shekaru biyu.
Okoronkwo, yace zai cigaba da bada hadin Kai ga kotun a duk lokacin da aka gayyace shi, ya kumayi kira ga Kotu da ta kori karar.
Chikere yace za’a dakatar da karar nan ba da dadewa ba, yanzu an dage zaman zuwa 7 ga watan Octoba don cigaba da Shari’a.