Gwamnatin Tarayya tace tana yin wani kokari na sanya kudaden da zata ware domin biyan tallafin Man Fetur a cikin Kasafin Kudi na Shekarar 2022.
Manaja-Daraktan Hukumar Kula da Man Fetur ta Kasa wato-NNPC Mele Kyari ya bayyana haka.
Gwamnati dai zata ware wannan zunzurutun kudi, duk da Dokar rarraba arzikin Man Fetur ta-PIA da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu, wadda zata rarraba bangaren Man Fetur.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wutar Lantarki ta kashe Dalibin Kwalejin Waziri Umaru Dake Birnin Kebbi
Gwamnatin Tarayya dai ta kiyasta ware Naira Biliyan 900 domin biyan kudaden Tallafin Man Fetur a Shekarar 2022.
Mr Kyari ya bayyana Haka a ranar Alhamis a lokacin wani taron na MTEF/FSP, Wanda Kwamitin Majalisar Dattijai akan Kudi ya shirya a Abuja.
A wani labarin Kuma na daban.
Jami’an Tawagar Yan sanda na jihar Niger dake yaki da Masu tada kayar baya, sun kashe hamshakin mai bai wa yan bindiga bayanan sirri Mai suna Buba Baromi, tare da wasu mabiyan shi 3, ya yin wani musayan wuta da ya afku tsakanin bangarorin biyu a garin Dogon Fadama na karamar hukumar Kontagora dake jihar.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, an kashe Baromi ne a maboyarvshi dake dajin Damba dake jihar.
Jami’an yan sandan sun kashe Baromi ne lokacin da yake tare da Mabiyasa a wani musayan wuta, da ya yi sanadiyar raunata wasu daga cikin yan bindigan.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, tawagar jami’an yan sandan dake yaki da masu tada kayar baya, sun farmaki maboyar Baromi ne karkashin jagorancin wani Mafarauci wanda jami’in sakai ne.
Wata majiya ta bayyana wa manema labarai cewa, An kashe Baromi ne a rana ta biyu da jami’an suka kai farmaki, ya yin da sauran mambobin shi aka kashe su tun a farmakin farko da rundunar yan sandan ta kai.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, Baromi ba bayanai kadai ke bai wa yan bindiga ba, inda ya kan jagoranci su zuwa Kai hari ko garkuwa da mutane a wasu yankunan na jihar Niger.
” Shine ya jagoranci satar Shanu, da kuma Kai harin garin Dogon Fadama a watan da ya gabata, wanda harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama wadanda basuji ba basu gani ba” inji majiyar
Sai dai duk yunkurin da mane ma labarai suka yi, domin ji ta bakin jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun, a bun ya citura.