Hukumar kula da dokokin hanya da ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta kara kudin bada lasisin amfani da Ada-daita Sahu, daga naira dubu 8, zuwa naira dubu dari.
Shugaban hukumar Baffa Dan’agundi ne ya bayyana wa manema Labarai hakan, a garin Kano.
Inda ya ce, “Ya kamata mu duba dukkannin aiyukan masu Adai-daita sahu sabida tsaro, inda muke bada na’urar bi-bi-ya kyauta, Amma bada lasisin ba kyauta ba ne.” Inji shi
Ya kara da cewa, “idan ya zama wajibi ka yi amfani da Adai-daita Sahu, to ya kamata kayi rajista” a cewar sa.
Kazalika ya ce, “Ya zuwa yanzu, hukumar ta ba da lasisin guda dubu sittin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar Dattijai ta shiga wata ganawar sirri da Ministan Mai da Mele Kyari
Dan’agundi ya kuma ce, hukumar ta KAROTA za ta wajabta wa Masu Adai-daita Sahu, biyan naira 100 kullun, a wuraren saida Tikiti, da hukumar kula da kudaden shiga ta jihar Kano ta kafa.
Ya Kuma yi kira ga dukkannin masu Adai-daita Sahu, da masu ababen hawa na haya, da su bi dokokin da hukumar KAROTA ta gindaya, Kuma su tabbatar an dauki bayanan ababen hawa su.
A karshe ya ce” idan su ka saba wa dokar za’akama su, Kuma a kurfanar da su” inji shi
Comments 2