Hadakar kwamitin kungiyar manyan malaman jami’o’i SSANU, da kuma kungiyar ma’aikatan jami’o’i NASU, sun tsayar da ranar Juma’a 5 ga watan Fabreru 2021, a matsayin ranar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin Nigeria.
Yajin aikin wanda zai fara bayan karewar wa’adin makonni biyu na yajin aikin gargadi da kungiyoyin suka shiga daga ranar Juma’a 22 ga watan Janairu, na zuwa ne kasa da wata daya bayan da kungiyar ASUU ta janye nata yajin aikin na watanni 9 da ta shiga.
Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, mai magana da yawun kwamitin hadin guiwar kungiyar SSANU da NASU, Peter Adeyemi ya ce gwamnatin tarayya ta cika alkawari daya ne kawai cikin shida da suka yi yarjejeniya akai a cikin watan Oktoba 2020, kuma a gaban ministan kwadago da daukar aiki ne aka yi wannan alkawari,
KARANTA WANNAN: Gwamna Bala Na Bauchi Ya Kulla Yarjejeniya Da Kamfanin Birtaniya Domin Samar Da Hasken Lantarki
Adeyemi ya ce yajin aikin ya samu amincewar kaso 89 na mambobin kungiyar NASU da kuma kaso 83 na mambobin kungiyar SSANU da kuma kaso 90 na kungiyoyin hadakar cibiyoyin jami’o’i ta Nigeria.
Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’in guda biyu sun gudanar da zanga zanga ta kwanaki 3 a makon da ya gabata domin jan hankalin gwamnati akan nuna bambanci wajen rabon N40bn da aka amince na alawus alawus da sauransu.