Akalla mutane 31,000 su ka yi rejistar daukar aikin da aka yi sanarwa na aikin koyarwa a makarantun gwamnatin jihar Osun, sai dai ana neman mutane 2,5000 ne kawai da za su yi aikin.
Daga cikin mutane 31,000 wadanda suka cike takardar bukatar neman aiki, mutane 29,000 ne kawai suka cire takardar da za ta basu damar rubuta jarabawar wannan aiki.
Kwamishinan ilimi na jihar Osun, Mr. Folorunsho Oladoyin, ya sanar da hakan a yayin da ya ke sa ido kan daukar aikin.
Oladiyon a cikin watan Disamba 2020 ya ce malamai 1,500 ne za a dauka aikin koyarsa a makarantun sakandire, yayin da za a dauki malamai 1,000 don koyarwa a makarantun firamare a fadin jihar.
Da ya ke tsokaci jim kadan bayan kammala jarabawar daukar aikin, Oladoyin ya bayyana gamsuwar sa kan yadda aka gudanar da jarabawar.
A cewar sa, hukumar zana jarabawar shiga manyan makarantu JAMB da aka baiwa alhakin gudanar da wannan jarabawar daukar aikin, ta samu goyon baya, ba tare da an yi mata katsalandan a ciki ba.
A cikin wata sanarwa daga Roselin Olawumi, jami’ar watsa labarai ta ma’aikatar ilimin jihar, a ranar Laraba, ta kuma ruwaito Oladoyin yana bayar da tabbacin cewa wadanda suka cancanta ne kawai za su samu wannan aiki.