Sabon karamin ministan ayyuka da gidaje Muazu Sambo ya yi ikirarin cewa ‘yan Najeriya za su yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kawai idan ya sauka daga mulki.
Sambo, wanda shugaban kasa ya rantsar da shi ne a ranar 24 ga watan Disamba a wata sanarwa a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga ma’aikatan ma’aikatarsa a Abuja, ya ce Buhari alheri ne ga Najeriya kuma masu sukarsa a yanzu za su sake tunani bayan ya bar mulki. a shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ofishin Babban Mai Binciken Kudi Na Tarayya Na Tuhumar NASS Bisa Zargin Karkatar Da Wasu Biliyoyin Kudi
“Na sha fada a baya kuma ina ta fadin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari alheri ne ga kasar nan. Na sha fada a baya kuma na sake cewa masu shakka ba za su gane haka ba har sai mai girma shugaban ya tafi.” Inji Sambo.
“Yan Najeriya da dama sun ki ganin kokarin shugaban kasa da ayyukansa nagari saboda ba sa yi masa adalci.
Sambo ya kara da cewa da a ce Buhari bai zama shugaban Najeriya a lokacin da ya hau karagar mulki ba, da kasar ta fada cikin halin kaka-ni-kayi saboda rashin gudanar da mulki da almundahana da gwamnatocin baya suka yi.