Wani gini mai hawa biyu dake yankin Ago Palace a jihar Legas ya sake ruftawa, a yau Asabar.
Dimokuraɗiyya ta samu labarin cewa mutanen dake zaune cikin daɗaɗɗen ginin, sun bar cikinsa lokacin da suka samu alamar cewa ginin zai iya ruftawa.
Shugaban Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar LegasDr. Olufemi Oke-Osanyintola ya ce basu samu labarin wanda ya jikkata ba, sakamakon wannan iftila’in.
Ya kara da cewa tuni suka mika ragamar kula da wajen ga hukumar ka da gine gine ta jihar Legas, domin daukar matakin da ya kamata.
Rushewar ginin dai ta faru ne da misalin karfe 3 na Asubar ranar Asabar, a yankin dake kusa da gidan man Kilimanjaro.
Jihar Legas dai na fama da yawaitar rushewar gine-gine a yan kwanakin nan, wasu ana tsaka da gina su, yayin da wasu kuma sun kwana biyu.
Comments 1