Yan majalisu na duba dokar yiwuwar sauke shugaban Kasa ko gwamna idan har ya sauya jam’iyyar daga wadda aka zabe shi. Kamar yadda Jaridar punch ta wallafa
A yanzu haka dai dokar na aiki akan Yan majalisun Jaha dana tarayya.
Wani Dan majalisa daga jam’iyyar PDP dan Jahar Taraba mai suna Rimamnde Kwewum, ya gabatar da wannan kudirin dokar ta fara aiki akan shugaban Kasa da gwamnan Jaha da mataimakinsa.
KARANTA:- Yan bindiga sun turo mana bidiyon yadda suka aurar da yaranmu, Iyayen daliban Kebbi
Tun daga dai babban zabe da aka gudanar a shekarar 2019 gwamnoni wadanda suka sauya shekar su zuwa wata jam’iyyar sun hada da gwamnan Jahar Ebonyi David Umahi, gwmnan Jahar Cross river Ben Ayade da kuma na kwanakwanannan gwamnan Jahar Zamfara Bello Matawallen Maradun.
Kudirin wanda a halin yanzu yana kan bita na biyu wajan Yan majalisun, ana bukatar sauya sashi na 144(1) da 189(1) na kundin dokar 1999. “Domin duba matsalar sauya jam’iyya dokar ta fara aiki akan shugaban Kasa da gwamna da mataimakinsa.
Kwemun lokacin da yake karin bayani cewa yayi “A hakin yanzu dokar sauke mutum daga mukaminsa na aiki ne kan Yan majalisu ne kawai, wannan na da bukatar a kara tsawon dokar don rike mutuncin jam’iyyar.”
“Babu shakka jam’iyyoyi ne kashin bayan Siyasa mai yanci, suna bada damawa mutane ta hanyar basu shawarwari, kuma tana taimakawa wajan ilimantar da yayan jam’iyyar.”
“Kuma ya kamata a girmama jam’iyyar domin ita ta basu shugabanci, don haka shugaban Kasa ko gwamna bazai sauya sheka ba kuma ya cigaba da mulki bayan wahalar da Jam’iyyar tasha dashi.”
Kamar yadda yan majalisun suka fada mutane sun zabi jam’iyya ne, shiyasa aka sanya alamar jam’iyyar akan takardar zaben.
Duk wanda yace zabe to wakilin jam’iyya ne. Kwawum yace.
Yace wannan yana da muhimmanci idan aka zabi mutum, shugaban Kasa ne ko gwamna ko mataimakinsa subar matsayin da aka zabe su, wannan ya nuna cewa basu iya Jagorantar jam’iyyar.
Comments 1