Wata Sabuwa: Zamu yi amfani da wasanni wajen Magance Talauci — Ministan Buhari
Ministan Matasa da Cigaban Harkokin Wasanni Sunday Dare yace Gwamnati a shirye take domin tayi amfani da wasanni wajen magance Talauci a Ƙasar.
Ya bayyana haka a Abuja a taron Asusun Kula da Caca karo na 13 – Rotary District 9125.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilan da suka sanya Ministoci, Masu Muƙami ke ruguguwar Kare Buhari — Femi Adesina
Yace Ma’aikatar tuni ta samar da wannan tsari dazai ciyar da Harkokin Wasanni a Matakin gaba, gami da inganta saka hannun jari wajen cigaban wasanni.
“Wasanni na ɗaya daga cikin abubuwan dake haɗa kan Al’umma Ƙasar nan. To muna so mu maido da kowa a ƙarƙashin Inuwa ɗaya domin yin amfani dashi wajen magance Talauci, yunwa, gami inganta ilmin bai ɗaya.
“Haka zalika, dai-dai ton jinsi za’a iya cim mashi ta hanyar wasanni tare da inganta zaman lafiyar kowacce Al’umma. A saboda haka, zamu ga canji daga matasa.”
Gwamnan kula da wanna District 9125 Ayoola Oyedokun yace a ƙarƙashin sa an samu cigaba.
Comments 1