Wani mutum ɗan kimanin shekara 41 da haihuwa ya harbu da cutar murar tsuntsaye a kasar Sin wato China, lamarin da ya sa ya zamo mutum na farko da cutar ta kama.
Ko da yake hukumomi ba su bada bayanan yadda aka yi mutumin ya harbu da cutar ba, amma an yi amannar cewa cutar mai samfurin H10N3 ba ta saurin yaɗuwa daga mutum zuwa mutum.
Kawo yanzu dai likitoci sun kammala jinya wa mutumin wanda asalin mazaunin Jiangsu ne, kuma tuni suka ce zai iya ce gaba da yawonsa duk inda ya ga dama ba tare da wata barazana ba.
Da ma dai a yan baya-bayan nan kasar China ta yi kaurin suna wajen wannan sabuwar cuta ta murar tsuntsaye, ko da yake har kawo yanzu babu wani rahoton cewa ma’aikatan dabbobin na iya kamuwa da ita.
Ita ma kasar Rasha ta bayyana a watan Fabrairu cewa cuta makamancin wannan ta bulla a kasar, to amma ta shawo kanta ba tare da wata-wata ba.