By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Asabar din data gabata ne wata motar tirela tafadi a kusa da kasuwar Suleja dake jihar Neja, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu.
Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 12:00 na rana, ya yi sanadiyyar lalacewar wasu motoci da ba a tantance adadinsu ba, da suka hada da babura uku da wasu motoci.
Wani shaidar gani da ido, Bala Saidu, ya ce jami’an tsaro da aka fi sani da ‘’yan gadi’ a garin ne suka tilasta wa direban motar sauya wurin da ya ajiye motar, inda suka zarge shi da yin parking din ba daidai ba.
Sa’idu yace: “Ya kai karar su kan matsalar tabarbarewar motar, amma basu saurare shi ba.
Bayan nan ne jami’an ‘yan banga na Masarautar suka kubutar da direban babbar motar daga hannun masu zanga-zangar inda suka mikashi ga jama’an ‘yan sandan dake yankin.
An kwantar da dukkan wadanda suka mutu a babban asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da wasu daga cikin wadanda suka tsira zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja,dake Gwagwagwala, domin kula da lafiyarsu.