Wata mata ‘yar ƙasar Indiya ta haifi ɗanta na farko tana da shekara 70 bayan ta amince tarte da mijinta zuwa asibiti domin ayi musu IVF (In vitro fertilisation) a karo na ƙarshe, hakan yasa ta zama mace ta farko da ta haihu tana da shekaru 70 a duniya.
Jivuпbeп Rabari da mjininta Maldhari, mai shekaru 75, ya nuna soyayya sosai ga ɗan nasu, wanda suka bayyana sunan sa ga manema labarai.
Rabari ta shaida wa manema labarai cewa tana da shekaru 70, wanda hakan ya sa ta zama mace mafi tsufa a duniya da ta haihu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cukon Mazaunan Da Tayi Ya Faɗo Tana Tsaka Da Rawa
Duk da haka, wata mata ‘yar Indiya, Erramatti Maпgayamma, ta ce an yi imanin cewa ita ce mafi tsufa bayan ta haifi ‘yan mata a watan Satumba 2019 tana da shekaru 74.
Jivuпbeп Rabari ta kasance bazata iya ɗaukan ciki da kanta ba, hakan yasa aka ɗauki ƙwan haihuwarta aka haɗa dana mijinta sannan aka mayar mata cikin mahaifarta.
Hakan yasa ta haife abinda ta haifa bayan kwashe waɗan nan shekaru.
Ya Rasu Bayan Da Aka Cire Masa Kodarsa Domin Sawa Mahaifiyarsa.
A WANI LABARIN KUMA: Wani matashi mai suna Muhammad wanda ya riga mu gidan gaskiya bayan da aka cire masa ƙodarsa domin a sakawa mahaifiyarsa.
Tun da farko dai mahaifiyar Muhammad ta kasance tana fama da ciwon ƙoda, hakan yasa likitoci a asibiti suka sanarwa da iyalanta cewar dole sai an canza mata ƙodarta sakamakon sun dai na aiki.
A ƙoƙarin ceto ran mahaifiyar tasa, Muhammad ya aminta ya bayar da tasa ƙodar guda ɗaya a sakawa mahaifiyar tasa.
Bayan gwaje-gwaje da likitoci suka yi, sun aminta da Muhammad ya bayar da tasa ƙodar domin a sanyawa mahaifiyar tasa.
Sai dai Allah cikin ikonsa, bayan da aka kammala aikin cire kodar ta Muhammad aka kuma sanyawa mahaifiyar tasa, sai Muhammad Allah ya yi masa rasuwa.
Ya rasu a lokacin da ita kuma mahaifiyar tasa take a raye yanzy haka.
Jaridar Zuma Times ce ta wallafa wanna\n rahoton a shafinta na sada zumuntar zamani ta Facebook.