Wata matashiya ‘yar shekara 16 mai suna Hamida Bawale ta nutse a cikin wata rijiya da ke unguwar kofar Fada Gidan Sarki a karamar hukumar Karaye a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai ranar Talata a Kano.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.
“Mun sami kiran gaggawa da misalin karfe 4:58 na yamma. daga ofishin jami’an tsaro na Civil Defence shiyyar Karaye, kuma mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 5:04 na yamma’’. A cewarsa.
Ya kara da cewa an fito da Bawale daga cikin rijiya da ta mutu, kuma an mika gawar ta ga dan uwanta Abdullahi Bawale na Kofar Fada Gidan Sarkin Karaye.
Abdullahi ya ce Bawale ya je dibar ruwa a rijiya, ta fada ciki.