Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna ya bayyana damuwarsa game yadda jihar take ci gaba da samun masu ɗauke da cutar sarke numfashi (Korona).
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da sashen BBC Hausa.
Gwamnan ya ce tabbas abun damuwa ne duba da irin alkaluman da ake samu a kullum daga cibiyar dakile cututtuka masu yaɗuwa NCDC ta fitar a ranar Juma’a.
“Ranar Juma’a za ka ga mutane sun yi cunkoso, to, idan muka ce za mu buɗe masallatan khamsus salawat wannan cunkoson zai ci gaba, ba a bin doka, ba a bin tsare-tsare,” in ji gwamnan.
A cikin kwana uku na baya-bayan nan kaɗai, cutar korona ta kama mutum 95 a jihar Kaduna, kamar yadda cibiyar NCDC ta bayyana.
Gwamnan ya ƙara da cewa jama’ar jihar basa bin dokokin da gwamnatin jihar ta gindaya, domin dakile cutar, sannan sun ci gaba da haɗuwa a wuraren cunkoso.
“Abinda ya fi ɗaga min hankali shi ne, kar a kai matakin da asibitocin jihar nan su kasa kula da masu ɗauke da cutar saboda tsananin yawansu” cewar El-Rufa’i.
https://dimokuradiyya.com.ng/zamu-iya-%c6%99ara-saka-dokar-kulle-a-kaduna-cewar-gwamna-el-rufai/
Har wa yau, Kasuwa na ɗaya daga wuraren da za a iya kamuwa da cutar cikin sauki, kuma idan wanda yake ɗauke da cutar ya shiga kasuwa zai shafawa mutane da dama wanda ba a san ta inda za a fara ba domin gano wanda suka harbu da cutar.
Haka kuma gwamnan ya koka kan yadda mutane ke ci gaba da rashin mutunta ƙa’idojin ba da tazara a wuraren ibada.
A baya dai, gwamnatin Kaduna ta sa dokar kulle fiye da tsawon wata uku kafin buɗe ta kuma yanzu haka jihar ita ce ta takwas a jadawalin jihohin Najeriya masu fama da cutar korona.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta buɗe wasu wuraren ibada da kasuwanni ba kamar a makwabtan jihar, abin da ya sanya mazaunan Kaduna ciki har da ‘yan kasuwa kokawa.
Elrufa’i dai ya ce maimakon ci gaba da buɗe jihar baki ɗaya akwai yiwuwar sake kullewa.