Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, ya bayyana watanni 18 da suka gabata a matsayin watannin da akafi shan wahala a tarihin Nigeria.
Buhari ya bayyana haka a jawabin da ya yiwa ƴan Najeriya, domin bikin murnar Ƙasar shekaru 61 da samun ƴancin kai.
“Watanni 18 sune waɗanda akafi shan wahala a tarihin Nigeria, domin ina ganin tun bayan yaƙin basasa, ina ganin da wuya in akwai lokacin da aka fuskanci matsalolin, fiye da wanda muka fuskanta a wannan lokacin,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babu wata Gwamnati tun shekarar 1999 da tayi abinda nayi a shekaru 6 — Jawabin Buhari na cikar Najeriya 61
Yace babban abinda gwamnatinsa ta sanya a gaba a shekarar 2020 shine cigaba da haɓɓaka tattalin arziki, biyo bayan karayar tattalin arziki da aka samu, sakamakon samar da dauwammen zaman lafiya da matsalolin tsaro dake fuskantar ƙasar.
Yace Matsalar cutar Covid-19, da matsalolin data haifar ga ƙasashe ya sanya kowacce gwamnati ta ɓullo da wasu sabbin dabaru.
Buhari yace gwamnatinsa na samun gagarumar nasara a yaƙi da matsalar tsaro.
Yace “a yayinda tattalin arzikin mu ya cigaba da dawowa bayan dokar kulle da cutar Covid-19 ta janyo, munga kuma dawowar matsalar tsaro a wasu sassan ƙasar.
“A watanni 4 da suka gabata, sojoji da sauran hukumomin tsaro, sun sami nasara mai yawa wajen yaƙi da matsalolin tsaro. Muna yaƙi da maƙiyan mu a dukkanin wani lungu da saƙo kuma muna samun nasara.