Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da a biya diyya ga duk wadan ya sami matsala bayan an yi masa allurar riga kafin corona. Shirin ya shafi kasashe kimanin 92 da ke fama da matsanancin talauci.
Biyan diyyan ya danganta ga wadanda aka yi wa allurar a karkashin shirin samar da magani na Covax. Lamarin da ake ganin ka iya kawar da shakku a tsakanin jama’a dama gwamnatoci a game da illolin da ake fargabar allurar riga-kafin cutar mai kama numfashi na iya haifarwa.
A daya bangaren kuwa, wani bincike na masana da aka gudanar a Britaniya, ya nuna yadda aka samu raguwar yaduwar cutar corona saboda tasirin allurar riga-kafin, wanda ke nufin zai matukar yin tasiri a sauran kasashen duniya, muddun aka rungumi tsarin yi wa al’umma allurar riga-kafin cutar.
A yankin Turai kuwa, gwamnatin kasar Italiya ta kara tsawaita dokar hana shige da fice a tsakanin kasar da sauran kasashe na yankin Turai. Sabuwar gwamnatin Firaiminista Mario Draghi, ta ce ta dauki matakin ne don shawo kan annobar cutar corona da ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar. Kasar ta ce za ta ci gaba da dokar kulle har ya zuwa ranar ashirin da bakwai na watan Maris mai zuwa.