Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadi game da amfani da maganin tari na Indiya guda biyu ga yara da ake kan karkara a Uzbekistan. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
WHO ta ce magungunan, wanda Marion Biotech ya kera, “na da karancin inganci” kuma kamfanin ya gaza bayar da tabbacin kare lafiyarsu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dandazon Jama’ar Da Suka Fito A Onitsha Ya Nuna Cewa, Peter Obi Ne Zai Lashe Zabe — COSEYL
Sanarwar ta zo ne makonni bayan da Uzbekistan ta yi zargin cewa yara 18 ne suka mutu bayan sun sha maganin da kamfanin ya yi amma har yanzu kamfanin bai ce uffan ba game da faɗakarwar.
Wannan dai na zuwa ne yayin da a cikin makon nan, sashen kula da abinci a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar inda kamfanin na Marion Biotech ke da cibiya, ya dakatar da lasisin kamfanin.
Majiyar Dimokuradiyya ta tuntubi Kamfanin hada magungunan na Marion Biotech da ma’aikatar lafiya ta Indiya don jin ta bakinsu.
Bayan da aka bayar da rahoton mutuwar mutane a Uzbekistan, ma’aikatar lafiya ta Indiya ta dakatar da samar hada magunguna a kamfanin.
A wannan makon, sashen kiyaye abinci a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar – inda Marion Biotech ya ke – shi ma ya dakatar da lasisin kamfanin.
Ko A watan Oktoba, WHO ta yi irin wannan faɗakarwa, tana danganta maganin tari guda huɗu da wani kamfanin Indiya ya yi da mutuwar yara 66 a kasar Gambiya.
Sia dai a wancan lokaci Gwamnatin Indiya da kuma kamfanin Maiden Pharmaceuticals sun musanta zargin.
A wnai labarin kuma, Ku Gayyaci Tinubu, Atiku, A Gwada Lafiyarsu, — Shehu Sani Ga NMA, NNNM
Tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani, ya yi kira ga kungiyar likitocin Najeriya, NMA, da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa, NANNM, da su gayyato dukkan masu neman takarar shugaban kasa domin a gwada lafiyarsu.
Sanata Sani ya ce hakan zai taimaka wajen daidaita cece-kucen da ake fama da shi a kan lafiyar wasu ‘yan takara a zabe mai zuwa.
Bayanin hakan na kunshe ne a wani sako da ya fitar ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Alhamis