A hukumance an ayyana bullar cutar Ebola ta baya-bayan nan a Kongo, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar Litinin din nan.
Hukumad ta ce barkewar cutar ta shafi lardin Equateur da ke arewa maso yammacin kasar, inda aka samu bullar cutar ta farko a ranar 23 ga Afrilu.
Ya ce a cikin dukka, an tabbatar da kamuwa da cutar mutane guda hudu da kuma mutum daya da ake zargi da kamuwa da cutar, amma majinyatan duk sun mutu ne sanadiyyar cutar.
A wata barkewar da ta gabata a lardin tsakanin Yuni zuwa Nuwamba 2020, an gano jimillar mutane 130 kuma mutane 55 sun mutu.
Koyaya, barkewar sabuwar cutar ita ce ta 14 da aka rawaito a cikin ƙasar mai mutane miliyan 90 tun 1976.
A tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, cutar ta barke a mafi girman garuruwa a yammacin Afirka inda sama da mutane 11,000 suka mutu.
Cutar Ebola takan haifar da zazzabi mai zafi da zubar jini a cikin jikk, kuma tana yin barazana ga rayuwa.
(dpa/NAN)
A wani labarin kuma daban
Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta kasa NAHCON ta bukaci maniyyata da su baiwa jami’an kasa da na jihohi hadin kai domin samun sakamako mai kyau daga gyare-gyare daban-daban na gudanar da aikin Hajjin bana.
Mataimakin ko’odinetan hukumar ta NAHCON a Makkah, Alhaji Alidu Shutti, ya bayyana haka a yayin wani taron tantance wuraren Mina, Arafat, Muzdalifa da Jamrat mai tsarki a birnin Makkah na kasar Saudiyya a ranar Litinin din nan.
Ya ce jami’an sun yi aiki da ma’aikatu daban-daban da aka tura Najeriya domin tsara jigilar maniyyata a tsawon kwanaki uku da za a yi a wurare masu tsarki.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa, Wurare masu tsarki, wadanda su ne muhimman abubuwan da ake gudanar da aikin Hajji, su ne wuraren da dukkan maniyyata daga sassan duniya za su ya da zango na tsawon kwanaki hudu kuma suna gudanar da wannan aiki a lokaci daya.
NAN ta kuma ruwaito cewa ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta bullo da wannan yunkuri ne domin rage yawaitar asara da cunkoson jama’a tare da kaucewa asarar rayuka a tsakanin alhazai.
Ya rage yawan maniyyatan da za su je jifan shaidan a Jamrat daga 250 zuwa 90 a lokaci guda daga kowace jiha.
Haka kuma an tsara lokacin da motocin bas za su isar da mahajjata daga Arafat zuwa Muzdalifa domin kwana a wani lokaci na dare.
Hakazalika, don tabbatar da ingantaccen tsari, hukumomin Saudiyya sun kuma gabatar da tarar Riyal 50,000 (kimanin Naira miliyan 11.5) da daurin watanni shida ga duk wanda ya yi aikin Hajji ba tare da izini ba.
Shutti ya ce hukumar ta NAHCON za ta tabbatar da cewa an yi wa maniyyatan hidima mafi kyawu a wurare masu tsarki.
“Makonni uku da suka gabata, hukumomin Saudiyya suna aiki a wadannan shafuka, kuma a yau, za ku ga bambanci, ko da lokacin da muka ziyarci ranar Litinin din makon jiya.
“ Wuraren kwana sun shirya; bayan gida an sabunta su, yayin da na’urar sanyaya iska kuma ke aiki.
“An ware wa alhazan Najeriya wuraren hidima daga daya zuwa na 18. Daya zuwa 14 an ware wa maniyyatan jahohi ne yayin da hudu kuma na masu yawon bude ido masu zaman kansu su yada zango.
“NAHCON za ta tabbatar da cewa maniyyata sun gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali,” inji shi.
Hakazalika, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta NAHCON a Madina, Dokta Hamidu Liman, ya bukaci maniyyata da su kasance cikin koshin lafiya na tsawon kwanaki biyar a wurare masu tsarki da sauran su.
“Hukunce-hukuncen aikin Hajji, kamar yadda kuka sani, sassarfa ne mai tsananin gajiya da tsauri. Muna nan don Ibada kuma dole ne mu yi, amma gwargwadon iko, dole ne mu sami lokaci tsakanin mu da huta da cin abinci mai kyau,” inji shi. (NAN)