Rahotannin da ke cewa Gwamna Nyesom Wike ya bayar da umarnin cire tutocin jam’iyyar PDP daga gidan gwamnati a Fatakwal karya ne , kamar yadda binciken DAILY POST ya bayyana.
A ranar Alhamis din nan ne dai aka rika yada jita-jita a shafukan sada zumunta cewa Gwamna Wike ya umarci babban jami’in tsaronsa da ya cire dukkan tutocin jam’iyyar PDP daga gidan gwamnati.
Sai dai binciken DAILY POST ya nuna cewa babu wata tuta da aka ciro daga gidan Brick House dake Old GRA a Fatakwal.
Wata majiya mai tushe daga fadar gwamnatin ta kuma tabbatarwa DAILY POST cewa rahoton ba gaskiya bane.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba shi da izinin yin magana a kan lamarin, ta ce duk tutocin da ke dauke da jam’iyyar PDP ba a taba su a gidan gwamnati ba.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/ku-samar-da-karin-magudanan-ruwa-a-jihohinku-fg-ta-bukaci-gwamnoni/
“Babu wani abu makamancin haka,” in ji majiyar.
An dai yi ta rade-radin cewa mai yiwuwa gwamna Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP saboda abokin burminsa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Wike dai ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a hannun Atiku, kuma an yi waje da shi wajen zaben wanda zai yi takarar mataimakin dan takarar shugaban kasar.