Daga: Abbas Yakubu Yaura
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gargadi magoya bayansa musamman jiga-jigan jam’iyyar da su daina furta kalaman tunzura jama’a da za su iya yin illa ga sulhun cikin gida da ake yi.
Wannan dai ya zo ne kamar yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da takwarorinsa na sauran jihohin kasar na aiki tukuru domin samun nasarar babbar jam’iyyar adawa a zaben shugaban kasa na badi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: Obasanjo, Wike, Obi Sun Gana A Birnin Landan
Atiku ya yi wannan kiran ne ta wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, a Abuja ranar Alhamis.
Matsayin tsohon shugaban kasar ya biyo bayan rahoton da kafafen yada labarai suka yi na cewa ana kara samun fargaba a jam’iyyar PDP na cewa rikicin da ke tsakanin Atiku da Wike na iya shafar damar sa a zaben shugaban kasa na 2023.
Har ila yau, a ranar Alhamis, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da Wike a birnin Landan.
Wike ya halarci taron tare da abokansa da suka hada da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo; Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue; Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke da dai sauransu.
Duk da cewa har yanzu ana kan zayyana cikakkun bayanai game da taron har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, jaridar The PUNCH ta samu labarin cewa wani bangare ne na tattaunawar da ake yi gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Sai dai Atiku a ranar Alhamis ya gargadi magoya bayan sa da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da su kau da kai daga yin kalaman da za su iya kawo cikas ga ayyukan da ake yi na kara karfafa jam’iyyar da kuma hada dukkan shugabanninta.
Sanarwar ta kara da cewa, “ya zama wajibi a yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar, shugabanni da duk wani mai alaka da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da su daina yin kalaman da ka iya rage kimar PDP.
“Wannan roko ya zama dole domin a jawo hankalin shuwagabannin jam’iyyar da mambobin jam’iyyar zuwa ga karkatar da jam’iyya mai mulki ta APC, wadda ke haifar da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP, da nufin karkatar da al’ummar Nijeriya su yi watsi da gazawar da aka samu na jam’iyya mai mulki.”
“A yau, ‘yan Najeriya sun zuba ido ga jam’iyyar PDP, domin ta jagoranci yunkurin kawar da jam’iyya mai mulki. Wannan fata da jama’a ke yi ne ya sa jam’iyyar APC ta yi kaca-kaca da faduwar su a babban zaben shekara mai zuwa. Wannan ne ma dalilin da ya sa jam’iyya mai mulki ke amfani da tsarin siyasa don haifar da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP.”
“Saboda sun san cewa babu abin da za su yi kamfen daga bayanan ayyukansu a ofis, jam’iyyar APC ta zabi ta taka rawar shaidan ne, inda suka yi bikin murnar rashin nasarar da suka yi a kan wata yaudarar cewa PDP ta rabu.
“Don haka na ke kira ga duk wani dan jam’iyyar PDP na gaskiya da kuma duk wanda ke fatan samun nasarar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da ka da su fada wa jam’iyyar APC ta maganganu da ka iya tabbatar da ikirarin karya na rarrabuwar kawuna. PDP.
“Dukkan shugabannin jam’iyyar da suka hada da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da dukkan gwamnonin jam’iyyar PDP sun hada kai wajen ganin jam’iyyar PDP ta samu nasara a babban zaben shekara mai zuwa a fadin kasar nan.
“Abin da ke tattare da zaben badi shi ne makomar Najeriya kuma dukkan shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar PDP suna kan manufa daya domin ceto Najeriya daga kangin da APC ta jefa su.”
A wani labarin kuma Uwargidan Obasanjo Ta Bukaci Gwamnatoci Da Su Tallafawa Masu Fama Da Ciwon Sukari
Uwargidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Misis Bola Obasanjo, ta bukaci gwamnati a dukkan matakai da su tallafa wa masu fama da ciwon suga a kasar nan.
Misis Obasanjo ta koka da cewa kudaden da ake kashewa wajen kula da ciwon suga na da yawa, inda ta kara da cewa majinyatan na bukatar taimako daga gwamnati da masu hannu da shuni.