Wike, Gwamnonin G-5 ba zasu iya hana nasarar Atiku ba – Segun Showunmi
Wani Jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Ogun Segun Showunmi ya bayyana Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da takwarorin sa na G5, basu da ikon hana nasarar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Alhaji Atiku Abubakar a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.
Showunmi yace Gwamnonin G-5, sun makance, suyi tunanin cewa, zasu iya hana ko su sanya ayi wani abu da ƙuri’un mabiyan su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Zai Bayar Da Kai Bori Ya Hau, Yana Shirin Ƙara Wa’adin Tsofaffin Kuɗi
Wike da Gwamnan Benue Samuel Ortom, da seyi Makinde na Jihar Oyo, da Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu na Jihar Abia, da Ifeanyi Ungwuanyi na Jihar Enugu, dukkanin su, basa Son nasarar Atiku, inda suka zabi kin goya masa baya, a dalilin Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayi ɗan arewa ne kamar Atiku.
Dagewar da da Gwamnonin na G-5 suka yi na cewa dole sai an sauke Ayu daga mukamin sa, a matsayin sa na shugaban jam’iyyar, ya maida Jam’iyyar baya, matsayin dalilin da ya sanya suka ƙi yiwa Atiku yaƙin neman zaɓe.
A wani labarin kuma: Kin Amsan Tsofaffin Kudi: Zanga-Zanga Ta Barke A Ondo
Gabanin zaben gama gari, jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) a jihar Filato ta narke cikin jam’iyyar, PDP. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Bayan haka jam’iyyar YPP ta ce za ta goyi bayan ‘yan takarar jam’iyyar PDP a dukkan matakai a babban zabe mai zuwa.