Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a ranar Asabar din nan ya tarbi daruruwan masu sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulkin kasa zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
Wadanda suka halarci taron a Fatakwal, babban birnin jihar sun hada da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Rivers, Desmond Akawor; tsohon dan kwamitin amintattu na jam’iyyar APC, Sam-Sam Jaja; tsohon kwamishinan wasanni, Fred Igwe; da daruruwan magoya bayansu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sauran tsoffin ‘yan APC da suka sauya sheka sun hada da Sylver Opusunju, Tele Betram Ikuru, Princewill Dike, Reginald Onwuka, Bestman Amadi, Amadi Nnokam, Muma Gift, Kennedy Ebeku.
A cewar gwamnan babban aikin da ya rataya a wuyansa shi ne tabbatar da cewa an zabe duk ‘yan takara a jihar Rivers a shekara mai zuwa.
Karanta kuma: Akwai Wani Da Yake Goyan Bayan Atiku A Fadar Shugaban kasa — Wike
“Jihar Rivers ita ce ta farko a gare ni kafin kowane mutum ko wata kungiya,” in ji Wike.
Ya kara da cewa “Dukkanku da kuka dawo cikin dangi, kuna da rawa guda daya da zaku taka domin fitowar dan takarar gwamnan mu.”
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Gwamnan ya ce wadanda suka sauya sheka sun zo ne a daidai lokacin da ya dace, inda ya ce zaben 2023 “ba na manyan mutane ba ne, ba na wadanda ba za su dawo gida su ja hankalin jama’a ba ne; suna sha’awar zama ‘yan siyasa ne kawai”.
Ya ce, “’Yan siyasa ana yin su ne a gida. Na canza dabarun wannan zaben – babu sauran manyan mutane. Ina zuwa ga waɗanda ke da mahimmanci a cikin raka’o’in su daban-daban.
“Duk wadanda suka yi murabus din su ne wadanda ba za ku ji sunayensu ba amma su ne suke yin aikin. Don haka, mun karbe su, kuma duk wadanda ake ce wa manyan mutane ana yi musu barazana.”
A wani labarib kuma: An Sanya Ranar Da Za A Yi Jana’izar Sarauniya Elizabeth A Watan Nan
Za a yi jana’izar Sarauniya Ingila Queen Elizabeth ta biyu a Westminster Abbey da ke Landan da karfe 11:00 na safe (10:00 GMT) a ranar Litinin, 19 ga watan Satumba, in ji jami’an masarautar a ranar Asabar din nan.
Fadar Buckingham ta kuma tabbatar da cewa Sarauniyar, wacce ta mutu ranar Alhamis tana da shekaru 96, za a kai ta zuwa St George’s Chapel da ke Windsor Castle, a yammacin London, don yin hidimar jana’izar.