A yunƙurin garambawul da kawo sauyi a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wikki Tourist dake Bauchin Yakubu da shahararre kuma gogaggen mai horas war nan yakeyi wato Usman Abdallah haifaffen jahar Kano wanda yake ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Wikki Tourist a kakar wasan data gabata.
A yanzu yana ta sayen manyan ‘yan wasa domin ganin ansami gyara na musamman a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Wikki Tourist, koda a kakar wasan data gabata saida ya sayi ‘yan wasa da dama a ƙungiyar ƙwallon ƙafan wanda kimaninsu yakai guda 10.
Sababbin ‘yan wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Wikki Tourist ta saya sune Andrew Abalogu wanda shine mai jagorantar ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba wato Captain da kuma Chinedu Udeagha daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Lobi Stars na garin Makurdi.
Shidai Udeagha yakan buga sashe da yawa idan yana filin wasa wato ba iya lamba guda yake bugawa ba duba da ƙwarewar da yake da ita ta musamman wajen murza leda, sannan shikuma Andrew Abalogu yakan kai kora wato ya taimakawa mai zura ƙwallo kenan, haka zalika shidai wannan ɗan wasa ya zauna a ƙarƙashin Usman Abdallah lokacin yana horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Enyimba International dake garin Aba.
Dukkanin ‘yan wasan guda biyu sun bayyana cewar burinsu shine su ga sun taimakawa ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Wikki Tourist sun sami tikitin wakiltar ƙasar nan ta Najeriya a kakar wasa maizuwa wato gasar zakarun nahiyar Afrika kokuma gasar ajin ƙwararru ta nahiyar Afrika wato Confederations Cup.
Wikki dai zatayi rigimar samun wannan tikiti a sabuwar kakar wasan gasar ajin Firimiya ta ƙasar nan da za a fara idan hikuma dake shiya gasar wato LMC ta sanya ranar da za a dawo sabuwar kakar wasa fil a leda wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021. Sai dai wasu suna ta yin ƙorafin cewa ya kamata a dawo buga gasar duba da yadda tuni aka fara fafata gasar rukuni-rukuni a nahiyar turai dama sassan duniya amma gasar ajin Firimiya ta Najeriya basu fara momai ba.