Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourist dake Bauchi ta nada Baba Jibrin a matsayin sabon mai horas da yan wasan ta.
Baba Jibrin ya mayw gurbin Usman Abdallah Shariff ne wanda ya ajiye aikinsa a jiya talata bayan shafe kaka guda yana horas da kungiyar.
Ko da yake har kawo yanzu Abdallah Shariff bai bayyana dalilinsa na ajiye aikin ba, amma wata kila haka bai rasa nasaba da irin halin niyasu da kungiyar ke ciki ne a kakar bana.
Shi dai sabon Kocin Wikki Tourist din Baba Jibrin zai kasance ne a matsayin mai rikon kwarya gabannin Ƙungiyar ta nada sabon mai horaswa na dindindin.
Baba Jibrin na daga cikin yan wasan Najeriya yan kasa da shekara 17 da suka fafata mata wasa a gasar cin kofin duniya ta Shekarar 1987.