Arsenal ta kammala siyan dan wasan Chelsea Willian a ranar Juma’a, bayan a yarjejeniyarsa da Chelsea na tsawon shekara uku ya zo karshe.
Dan wasan mai shekara 32, ya zo Arsenal ne a kyauta. Kafin zuwansa, ya lashe gasar Firimiyar Ingila sau biyu, da kuma kofin kalubale na FA, da kuma League Cup, da kuma kofin Europa na tsawon shekara bakwai a zamansa da Chelsea.
“Na yi imanin cewa dan wasa ne da zai kawo mana sauyi.” Inji Kocin Arsenal, Mikel Arteta. Ya ci gaba da cewa; yana da kwarewa a fannin wasan kwallon kafa na duniya, amma yana da burin ya zo Arsenal domin ba da na shi gudummawar. “Na ji dadi da duka tattaunawar da aka yi da shi akan son zuwansa nan.” Inji Arteta.