Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Wasu hotuna da suka rinka yawo a dandalin sada zumunta, na Adamar Kamaye tare da wani da a ke tunanin mijin ta ne, da za ta aura ya tayar da Kura a yan kwanakinnan.
Ba komai ya sa hotunan suka tayar da Kurar ba, sai don kawai an ga hotunan ba, tare da wani karin bayani ba, don haka ne ma wasu suka rinka yanke hukuncin cewar Adamar Kamaye za ta auri wani yaro ne.
To sai dai a tattaunawar da wakilin Jaridar Dimukaradiyya ya yi da ita fitacciyar Jarumar Hajiya Zahra’u Sale, wacce aka fi sani da Adamar Kamaye, ta bayyana mana cewar.
“Gaskiya hotunan da aka rinka gani nawa da wannan Yaron ba auren sa Zan yi ba, domin kuwa a zahiri ma shi da ne a gare ni.” Inji ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga Sun yi garkuwa da wata mata da Ya’yanta Biyu a Kwara
“Amma dai abin da ya faru shi ne, a yanzu na samu wata dama ce da a baya ban same ta ba, domin a baya ni jaruma ce fim na ke yi ina fitowa a matsayin jaruma, to a yanzu ina son na shirya fim nawa na kaina, wanda na saka masa suna Matar Yaro. To wannan ce ta sa muka dauki wannan hotunan da shi, wanda zai fito a matsayin mijina a cikin fim din, muka yada shi a duniya, su kuma mutane har suka rinka yanke hukunci a kan zan yi aure ne, to gaskiya fim ne zan fara nan gaba kadan za a shiga aikin fim din” a cewar ta.
Kazalika Adamar Kamaye ta roki masoyan ta, da su taya ta da addu’a, domin samun nasarar akin fim din da za ta yi.