Wasu ‘yan uwan juna biyu sun yi matsanancin kone wa sakamakon fashewar wani ma’ajiyar kananzir a karamar hukumar Obubra da ke jihar Cross River.
Mahaifin wadanda abin ya shafa, Mista Washington Udoh, wanda limamin coci ne, ya ce fashewar ta auku ne a makon jiya da yamma a harabar cocin inda ya nemi mafaka, sakamakon rikicin kabilanci da ya barke tsakanin mutanen Ochon a Obubra da Alesi a Ikom. Inda nan ma rikicin yayi sanadiyar asarar wasu rayukan.
Udoh ya ce, “Ban nan a lokacin da lamarin ya faru amma makwabta sun ceto ‘ya’yana masu shekaru 11 da 13 a madadina. Ina tsammanin Cocin ya fi aminci lokacin da na tsere daga rikicin kabilanci a yankin.
“Konewar ta yi tsanani. Sun kasance a babban asibitin Obubra inda suke karbar magani.”
Ya roki jama’a da su ba su tallafin kudi, ya kara da cewa likitocin na iya nemansa ya kai ‘ya’yansa gida saboda tsadar rayuwa.
Ya yi kira ga gwamnati da ta dakile fasa-kwaurin albarkatun man fetur a jihar.