Wutar Lantarki ta Hallaka Wani Dan Karambanii a Edo
Onyenka Augustin mutum mai shekaru 42 ya sheka layira wajan yin karambanin mai da wayar wutar Lantarki bayan masu aikin sun yanke masa.
KARANTA:- Ka Zama Zakaran Gwajin Dadi, Gwamna Yahaya Bello
Mai magana da yawun Yan sanda na Jahar Edon SP Kotongs Bello yace Lamarin ya aukune a ranar Juma’a da misalin karfe biyar a 6, Akube Street a Birnin Benin.
Kamar yadda aka ruwaito an yanke wutar Lantarki gaba daya layin Eguavoen dake Benin.
Jim kadan bayan aukuwar lamarin lokacin da Yan sanda suka kawo taimakon gaggawa suka cimma gawan sa a saman wayar wutar Lantarki yana lilo.
Kamar yadda aka ruwaito Yan sanda suka sauko da gawan sannan suka mikata gidan mamata.
Yan sanda sunyi bakin kokarin su wajan an nemo Iyalan marigayin.
Shugaban Yan sanda dake jahar ya gargadi Mutane dasu rage karambani da miyagun ayyuka don ba abunda yake haifarwa sai Asara.
A yunkurinsa na tabbatar da an dakile miyagun ayyuka a Jahar Edo wannan bayani nada matukar anfami ayishi.
Kwamishinan Ƴansandan yace mutane dasu cigaba da bayyanama Yan sanda da labarai nagari don gani sun kawo dauki.