Wani dalibin Mai shekara 24 na Kwalejin kimiyya da fasaha ta Waziri Umaru dake Birnin Kebbi a jihar Kebbi, Mai suna Khalid Kabir Argungu ya mutu har lahira sanadiyar wutar Lantarki a dakin kwanan dalibai na makarantar.
A cewar rahotonnin da jaridar Dimokuradiyya ta samu, lamarin ya faru ne, ya yin da dalibin ke kokarin cin abinci.
Lokacin da yake tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai, Shugaban Makarantar Muhammad Aliyu, ya bayyana cewa, Likitoci da malaman jinyan dakin Shan magani na Kwalejin, sun yi gaggawan Kai dabibin asibitin Sir Yahyah dake garin Birnin Kebbi, lokacin da suka ga jiki shi ya yi tsanani, inda daga bisani ya rugamu gidan gaskiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an yan sanda sun kashe kasurgumin Mai bai wa yan bindiga bayanai a Niger
Kazalika Shugaban makarantar a cikin yanayi na jimami ya ce, hukumomin Kwalejin sun sanar da Iyayen dalibin dangane da abun da ya faru, inda ya ce, sun Kuma bukaci da akai gawar Mamacin zuwa mahaifar shi na Argungu, domin yimai jana’izar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ya kara da cewa, “Mun kaddamar da kwamitin domin bincike kan mutuwar dalibin, Kuma da zaran kwamitin sun kammala binciken su, zamusan me za mu yi nan gaba, domin hana sake afkuwar hakan”
.
A karshe shugaban makarantar ya kuma yi watsi da jita-jita cewa, hukumomin makarantar sun kulle Kwalejin.
Comments 1