Hukumar samar da wutar lantarki ta kasa ta gamu da koma baya a yau Talata, sa’o’i 24 bayan da wata na’ura da suka kafa ta ruguje, wanda hakan ya haifar da katsewar wutar lantarki.
Sabon tsarin ya gamu da tazgaro ne tsakanin karfe 5 na yamma zuwa karfe 6 na yammacin yau Talata, Ƙarfin wutar lantarki ta ragu daga megawatts 3,000 a baya zuwa Megawat 1,758 wanda hakan ya sanya kamfanoni 12 na bayar da hasken lantarkin ne kawai suke aiki.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani rahoto da ke nuna cewa kamfanin raba wutar lantarkin ya samar da wutar, kamar yadda yake bisa ga bayanan sa’o’i da sashen sadarwa na kamfanin (TCN) ya bayar.
Wani jami’in masana’antu ya kuma tabbatar da cewa rugujewar tsarin na yau ya yi muni, musamman daga tasoshin wutar lantarkin da ake amfani da iskar gas yayin da ake kokarin samar da wutar lantarki zuwa Abuja, babban birnin Najeriya ta hanyoyin samar da wutar lantarki guda uku.
Magudanan ruwan da akan samu wutar yanzu haka sun hada da Kainji, Jebba da Shiroro duk a kasar Nijar.
Ministan wutar lantarki, Engr. Abubakar D. Aliyu, ya gabatar da wani taron gaggawa inda ya dorawa alhakin aikin ga ma’aikatan aikin hadin gwiwa domin ganin an samu kwanciyar hankali.
Aiyu ya ce: “An kira wannan taro ne domin magance matsalar wutar lantarki a kasar nan wanda ba mu ji dadinsa ba. Dole ne mu nemo mafita ta yadda ’yan Najeriya za su samu wutar lantarki. Ina so mu yi hakuri mu tattauna da juna, ba wai muna zargin junanmu ba”.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne Kamfanonin rarraba wutar suka koka kan rashin samun kudaden shigar da ake samu wajen samar da iskar gas da kuma al’amuran fasaha da galibin sassan masana’antun da ake harba iskar gas da aka ce suna karkashin kulawa.