Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona kuma ɗan asalin ƙasar Andalus wato Xavi Hernandez yanaci gaba da kafa tarihi a matsayinsa na mai horas wa tun bayan da ya rataye takalmansa ya kama aiki a matsayinsa na mai horas wa. Kuma alamu sun nuna yana ta samun nasarori kamar yadda ya samu a lokacin da yake murza leda.
Xavi dai ya koma can ƙasar Qatar yana horas da wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa inda ya zuwa yanzu ya kwashe watanni 12 wato shekara guda kenan a matsayinsa na mai horas wa a can ƙasar ta Qatar kenan. Shidai Xavi yana horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Sadd dake can ƙasar ta Qatar.
Ya zuwa yanzu Xavi ya jagoranci ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Al Sadd ta lashe kofuna guda uku tun bayan da ya fara horas da ita wanda koda a makonnan ya jagorance su sun buga wasan ƙarshe kuma sun lashe kofin inda suka lallasa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Arabi daci 4 da nema awasan na ƙarshe da suka buga.
Xavi dai ya lashe kofi mai taken Qatar Super League da Qatar Cup da kuma Qatar Supercup, lokacin da Xavi yaje ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Sadd tana da kofuna 69 a tarihi data lashe, yanzu kuma ya jagoranci ƙungiyar ta lashe kofuna guda 3 inda jimilla ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Al Sadd ta lashe kofuna guda 72.
Shidai Xavi Hernandez ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta nuna sha’awarta ta ya fawo ya jagorance su amma kuma yace a’a duba da yadda yaga ƙungiyar tana cikin ruɗani da fargaba da kuma rikici dangane da yadda akesa ran za a shawo kan matsalolin ƙungiyar ƙwallon ƙafan na yadda zata koma dai-dai kamar yadda take da.