A yayında ƙasashen da suka ci gaba ke rige-rigen samo rigakafin annobar Korona, nahiyar Afrika na tafiyar hawainiya,duk da ɗakunan gwaje-gwaje da aka samar da nufin daƙile cutar.
Nahiyar Afirka ta ga ci gaba da kuma koma baya a yaƙi da Korona. A wannan makon, jami’ai sun yi marhaban da buɗe cibiyar sadarwa ta ɗakunan gwaje-gwaje masu tsara ƙwayar halitta.
Daraktar nahiyar Afirka ta hukumar lafiya ta duniya WHO, Dr. Matshidiso Moeti, ta sanar a jiya Alhamis cewa WHO da kuma hukumar daƙile cuttuka masu yaɗuwa ta Afirka sun buɗe ɗakunan gwaje-gwaje 12 a nahiyar don yin aiki kan tsarin ƙwayar COVID-19 da kuma nazarin bayanai.
Ta ce “Wannan hanyar sadarwar za ta taimaka mana wajen bin diddigin yadda ƙwayar cutar take yaɗuwa don samar da allurar rigakafi da kuma magunguna da suka dace da mutanen Afirka. Kuma hakan zai taimaka mana ya zama mun wuce gaba a yaƙi da cutar Korona.
Sai dai kuma duk da wannan ci gaba, an samu koma baya. An dakatar da gwajin allurar rigakafin na farko, da ake yi a Afirka ta Kudu.
Babban kamfanin harhaɗa magunguna na Birtaniya da Sweden Astra-Zeneca ya sanar a wannan makon cewa dakatar da gagarumin gwaje-gwajen allurar rigakafin Korona saboda wani wanda ya shiga cikin shirin a Birtaniya ya kamu da rashin lafiya bayan karɓar magungunan gwajin.