Majalisar Dattijai a ranar Talata, ta tabbatar da Mr Yahaya Muhammad, wani da za’a naɗa a Hukumar gudanarwar hukumar hana zagon ƙasa wato EFCC, wanda bayanan daya bayar suka nuna cewa ya fara makaranta kafin a haifeshi.
Muhammad na ɗaya daga cikin mutane biyar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya turawa majalisar domin tantance su a ranar Talata.
Tabbatar da tantance su ya biyo bayan wani rahoto da kwamitin majalisar akan yaƙi da rashawa ya bayar, ƙarƙashin jagorancin Sanata Suleiman Abdu Kwari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Enugu Ta Dakatar Da Wani Mahaifin Basarake
Buhari a takardar daya aikewa majalisar mai kwanan 17 ga watan Satumba na shekarar 2021, ya buƙaci majalisar ta tabbatar da naɗin sakatare da sauran hukumar gudanarwa na hukumar hana zagon ƙasa.
Waɗanda aka tantance tare da Muhammad sun ƙunshi George Abang Ekungu a matsayin sakatare, wanda ya fito ne daga Cross River, sai Luqman Muhammad daga jahar Edo, da Anumba Adaeze daga jahar Enugu da kuma Kola Raheem Adesina daga jahar Kwara.
Sanata Kwari a jawabinshi, yace kwamitin ya duba dukkanin takardun su ya kuma amince da saninsu da ilminsu da iyawar su, domin haka zasu iya gudanar da aikace-aikacen da aka ɗora masu.
Yace Babu wani rahoto ko wani ƙara akan kowane daga cikin su, sai ya buƙaci sanatoci dasu amince dasu.
Amma a nashi jawabin, Sanata Hassan Hadejia ya janyo hankalin majalisar data duba cewa, rahoto ya nuna cewa an haifi Muhammad a ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 1969, amma ya fara makaranta a shekarar 1968.