Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywwod Hannatu Bashir wadda aka fi sani da Hanan, ta yi Kira ga Jama’a musamman masu kallon su da su dinga kyautata musu zato a Kan sana’ar su.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa, Jarumar ta ce “Ni a matsayina da nake harkar fim Ina son mutane su yi mana kyakkyawar mu’amula, Kuma Kullum su rinka kyautata mana zato.
2023: Dalilin da Yasa Ba zan Yi Murabus Ba, Ministan Buhari Ya Yi Zazzafan Martani
A duk lokacin da suka kyautata mana zato za mu ji dadin hakan, saboda kusan Abubuwan da su ke fada a gare mu da yawa ba halin mu ba ne zargi ne kawai su ke yi.”
Ta kara da cewa ”Mu akankin kanmu, mu iya bakin kokarin mu wajen kiyaye dokar Allah, a matsayinmu na Musulmai.
Don haka muna Kira ga Jama’a da su daina yi mana mummunar fahimta a rinka daukar mu a matsayin ƙanne kuma ƴaƴa a gare ku, ta haka ne za mu rinka karbar duk wani gyara da aka yi mana ba ta hanyar cin zarafi ba,” inji Jaruma Hanan.