Ya kamata tun farko masu adawa da Tinubu su taimaki Kirista ya samu tikitin APC – Oshiomhole
Adams Oshiomhole ya zargi wasu Jiga-Jigan Kiristoci da jagorantar yin adawa a kan Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu a yayin da ake tunkarar Zaɓen 2023.
Tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Ƙasa ya ce sukar da ake yi wa tikitin Musulmi da Musulmi abin takaici ne.
Oshiomhole ya shaidawa Manema Labarai a Abuja ranar Alhamis cewa matsalolin Najeriya sun fi rashin jituwa kan Addini.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yajin aiki: A bayyane yake FG, ASUU babu abin da za su yi asara — Ƙungiyar Ɗalibai
Tsohon Gwamnan Edo ya bayyana matsayin masu sukar Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu a matsayin bakar fata ce kurum.
“Wadanda ke jagorantar yakin neman zaben a cikin APC – inda waɗannan ne da suka yi amanna da Kiristanci -da sun sami damar nemo ƙuru’u a cikin ƴan takara Kirista.
“Amma sun kasance a rubuce cewa sun jagoranci yakin neman zaben a bangaren Asiwaju Bola Tinubu, da sanin cewa shi musulmi ne,” in ji shi.
Tsohon shugaban Ƙungiyar Ƙwadagon ya bayyana cewa kalubalen Najeriya ya wuce addini.
“Batutuwan da za mu dauki lokaci muna tattaunawa su ne abin da kowane dan takarar shugaban kasa zai yi daban, ba wai abin da Kirista ko Musulmi zai yi ba,” inji shi.
Oshiomhole ya kuma caccaki ikirarin cewa ana tsananta wa Kiristoci, yana mai cewa babu wata shaida a kan haka.
“Ba na tsammanin zasu iya nuna shaidar amma duk da haka bawai Mataimakin Shugaban Kirista kawai ke garemu ba, muna da Fasto”, in ji shi.