Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman ‘yan Deltan da su kara saka hannun jari a harkar noma.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa wannan a ganin gwamnan na a matsayin hanyar dakile matsalar karancin abinci a Najeriya da samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki ga al’umma.
Okowa ya yi wannan kiran ne bayan ya duba aikin noman dabino da matatun mai da ake ginawa a Akwukwu-Igbo, karamar hukumar Oshimili ta Arewa da Northsworthy Farms and Allied Industries Limited tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar.
Ya ce noman dabino yanki ne da ’yan Deltan masu hannu da shuni ke ci gaba da zuba hannun jarin su don bukasarsa.
KARANTA ANAN: Buhari Zai Halarci Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo Na 77
‘Yan Najeriya za su iya saka hannun jari don samar da ayyukan yi, yana mai cewa sun yi nasarar dasa itatuwan dabino sama da 250,000 a sama da hekta 1,400 na kasa, ya ce ya yi imani da wannan hadin gwiwa domin zai taimaka wa al’umma na kusa da muhalli.
Okowa ya ce shekaru hudu da suka gabata mahukuntan Norsworthy Farms sun yi magana da shi lokacin da za su fara aiki, kuma hakan yasa ya ga dacewar gwamnatin jihar ta ci gaba da tallafa musu tare da hada hannu da su wajen bunkasa wannan noman na dabino.
A wani labarin kuma: Dubban Mambobin APC Ne Suka Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar PDP A Kaduna
Sama da mambobin jam’iyyar APC 13,000 ne suka fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar PDP, a Kudancin Kaduna.
Ma’ajin jam’iyyar adawa ta Arewa maso Yamma, Hon. Rabiu Bakori, wanda ya karbi sabbin mambobin a madadin shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma, Sen. Hayatu Gwarzo, a yankin Zonkwa, ya ce idan har jam’iyyar ta ci zabe a 2023 dole ne kowa ya tashi.