Ya Saɓa Doka Gabatar Da Masu Laifi da Ƴan Sanda da wasu Ke yi – NHRC
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa NHRC, ta ce ba bisa ka’ida ba, kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, rundunar ‘yan sandan Najeriya, da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, da sauran hukumomin tsaro su gabatar da wadanda ake tuhuma da ba a hukunta su ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Anambra ta rufe otal saboda bikin Jima’i
Da yake zantawa da manema labarai jiya Alhamis a Abuja, babban sakataren hukumar ta NHRC, Tony Ojukwu, ya ce hukumarsa za ta dauki matakin shari’a a kan ‘yan sanda da sauran hukumomin da ke da hannu a lamarin.
Ya kara da cewa har kotu ta yi Allah-wadai da matakin gurfanar da wadanda ake tuhuma gabanin shari’a.
Ya kuma yi kira ga duk wanda ake tuhuma da aka gabatar gaban shari’a da ya kai karar hukumar, inda ya tabbatar da cewa za a ci gaba da shari’ar.
“Abin takaici, mun gano cewa mutanen da aka tauye hakkinsu ta wannan hanya, suna tafiya suna mantawa da komai da zarar an bayar da belinsu.
“Bari in sanya a rubuce cewa duk wanda aka yi wa irin wannan halin zai iya tuntubar hukumar kuma tare, za mu bi diddigin lamarin har sai mun samu adalci.
“Duk da haka, idan bayan an kama wani kuma mutumin ya tafi ba tare da bin shari’ar ba, ba zai yuwu a magance lamarin mutumin ba.”
Ojukwu ya kuma ce hukumar za ta hada kai da masu ruwa da tsaki domin ganin an kare ‘yan jarida.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Abuja, Emmanuel Ogbeche, ya ce akwai bukatar a samar da wata doka ta kare lafiyar ‘yan jarida.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Buhari ta buƙaci Jami’o’i dasu tarawa kan su Kuɗaɗe ta hanyar neman tallafi
A ranar Alhamis ne Gwamnatin Tarayya ta buƙaci Majalissar gudanarwar Jami’o’i da su nemi tallafi daga Ƙungiyoyin Agaji da ɗaiɗaikun mutane domin samun ƙarin kudaden gudanar da ayyuka.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayar da wannan shawarar jiya a Abuja, yayin da yake kaddamar da majalisar gudanarwar jami’ar noma ta tarayya dake Abeokuta; Michael Okpara University of Agriculture, da Jami’ar Noma ta Umudike; Joseph Sarwuan Tarka University of Agriculture, da Jami’ar Noma ta Makurdi da ta Zuru