Wani matashi ya sha kuma bayan kai wa budurwarsa ziyarar ba zata inda ya ga abinda yayi matukar daga masa hankali har ya kasa hakuri yayi wallafa a soshiyal midiya, Legit.ng ta ruwaito.
Wannan wallafar ta sa mutane da dama sun dinga kwanta masa da hankali inda su ka ba shi shawarar ya bar ta ya ci gaba da rayuwarsa.
KU KARANTA: Yadda Sule ɗan achaɓa ya cika bujensa da iska bayan budurwar da su ke lalata ta sheƙa lahira
Ya wallafa hirar ne a Twitter inda yace bayan isar sa gidan ba tare da sanar da ita ba, ya dade yana kwankwasa kofa amma be ji amsa ba.
Wannan dalilin yasa ya koma ta kofar baya inda ya hango wani namiji yana kokarin tserewa daga gidan kamar yadda ya bayyana.
Ya ce:
“Ina cikin hawaye. Ina fama da radadi a zuciyata. Na je wurin budurwata da safen nan. Kawai na kai mata ziyarar bazata. Yayin da na dinga kwankwasa mata kofa ba tare da ta amsa ba. Na zaci tana bacci ne.
“Wannan dalilin yasa na tafi ta kofar baya. Kawai sai naga wani namiji yana lallabawa ta kofar baya yana so ya tsere. Wannan ya yi matukar hassala zuciyata.
“Nan da nan naji saukar hawaye daga idanu na. Na kusa tafka hadari a hanyata ta komawa gida.”
Yayin da wasu ke ba shi hakuri, wasu sun ce ya yi hanzarin yanke hukuncin ta yuwu ba abin da yake tunani bane.
Wasu kuma sun kwantar masa da hankali tare da ba shi shawarar ci gaba da rayuwarsa.
Yadda budurwata ta rabu dani bayan na yaba da kyawun hoton wata budurwa a Facebook, Matashi
Wani matashi mai suna Ade ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi bayan ya yi sharhi kan hoton wata budurwa, LIB ta ruwaito.
Ya wallafa hakan ne a Facebook a wani rukuni ranar Talata, 22 ga watan Nuwamban 2022.
Kamar yadda ya shaida, budurwarsa ta hassala ne bayan ganin sharhinsa karkashin bidiyon wata hakan yasa ta hukura da tarayya da shi.
A cewarsa, ba wani dogon sharhi yayi ba, kawai ce wa budurwar yayi ta yi kyau.