Wata Santaleliyar Budurwa yar Najeriya ta bayyana wani abin al’ajabi da ya faru da ita a kwanakin baya, bayan da wani da ba ta san ko wanene ba ya tare ta a bakin hanya yana so ta mishi kwatance.
Budurwar mai suna Oluwaseun Ayodeji Osowobi ta ce wani bako ne da bata san ko wanene ba ya tare ra a hanya yana tambayata hanya, sai dai daga fara Mishi Kwatancen sai ta ji tunanin ta ya gushe.
Ta ce ba ta san ya aka yi ba kawai ta rinka bin shi kamar kare da mai shi, ba tare da wata-wata ba sai ganinta ta yi a dakin shi.
Wani karin abin al’ajabi a cewar matashiyar shine, yadda ya umarci ta da ta je gida ta tattaro dukkanin sarkoki da yan kunnen mahaifiyarta ta kawo Mishi, to amma da yake Allah ba azzalumin kowa ba ne, gabannin isar ta gida kwatsam sai ta ji ta dawo hayancin ta.
“Ba zan taɓa mance lokacin da wani ya tare ni wai na mishi kwatance ba, kwatsam ina farawa sai na ji na fita a hayaci na, sai ga ni a dakin shi”
“Ina zaune na kura mishi idanu sai ji na yi ya ce mun tashi ki je gida ki dauko akwatin sarkoki da yan kunnen maman ki”
Na fita ina cikin tafiya kenan sai na ji na dawo hayaci na, yanzu da ya kashe ni a wurin fah? Ya Allah ka tsare mu” Cewar ta.
Ko da yake ba kasafai ake samun abubuwan mamaki da al’ajabi irin wannan a Najeriya ba, to amma wani zubin hakan na faruwa ne sakamakon irin kwadayi na yan matan wannan zamani.
Yayin da a hannu guda kuma faruwar hakan na biyo bayan irin umarni ne na masu gidan masu aikata hakan ma’ana masihirta kenan, to sai mu ce Allah Ya kare.