Ya zama dole ASUU ta biya diyya ga Ɗalibai kan ɓata masu lokaci – Minista
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, a ranar Alhamis din da ta gabata, ya ce alhakin Ƙungiyar malaman jami’o’i ne ta biya daliban da suka ɓata wa lokaci a yajin aiki na watanni shida, ba Gwamnatin Tarayya ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ƙungiyar Lauyoyi ta fusata, tayi maganganu kan goyawa Ɗan Takara baya
Ya kuma ce Gwamnati ba za ta amince da buƙatar kungiyar na biyan malamai kudaden alawus-alawus din su na tsawon watanni shida ba tare da koyar wa ba.
Adamu ya ba da shawarar cewa daliban da abin ya shafa su kai ASUU Kotu domin neman diyya da aka yi a lokacin yajin aikin.
Ministan Ilimin ya bayyana haka ne a wajen zama na 47 na taron Manema Labarai na Majalisar Dokokin Jiha da tawagar Shugaban kasa kan sadarwa ta shirya a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ba ta da wani alhaki na biyan miliyoyin daliban da aka dakatar na tsawon watanni shida saboda bata lokaci.
Ya kuma ce idan daliban sun kuduri aniyar samun diyya to su gurfanar da ASUU a kotu.