Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya sake jaddada bukatar jama’a su guji rarraba addini da rashin fahimtar juna a tsakanin daidaikun mutane.
Akeredolu ya nanata matsayarsa kan shugabancin Kudancin kasar, inda ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a mika mulki ga yankin Kudu domin tabbatar da adalci, daidaito da kuma gaskiya.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin nan a babban taron Cocin kasa da kasa na Agape karo na 34 a Akure. Jigon taron shi ne: “Wannan ne Lokaci na.”
Ya kuma jaddada cewa al’umma sun kasance tare da juna duk da bambancin addini a baya.
A cewarsa, muna da daidaituwa mai ban sha’awa a nan. A yau, muna tare da mai girma Omolewa, matar tsohon Gwamnan jihar Kwara a nan.
“Na san ta Kirista ce ta gaskiya, mai gaskiya ce, tana jagorantar bagadi a gidanta, a gidan da mijin kuma Musulmi ne na gaske. Kuma dukkansu suna zaune lafiya.
“Akwai mutane da yawa a nan da suke da Musulmi da Kirista a matsayin ’yan uwa kuma babu jayayya. Kada addini ya kawo rigima a tsakaninmu kuma a nan ne muka tsaya.
“Abin da muka yi imani da shi, kuma muka tsaya tsayin daka shi ne, tun lokacin da muka fara wannan jamhuriya a 1999, muna ta karba-karba daga Arewa zuwa Kudu, kuma a gare mu, a wannan lokacin, lokacin Kudu ne.
“Wannan shine lokacinmu kuma babu wanda zai dauka. ‘Awa lokan’. Babban jigo na wannan lokacin. Lokacin da aka zaɓi jigon, na tabbata ba wanda ke tunanin ‘Emi loka’ ko wani abu; amma ta hanyar kwatsam ne kawai.
“Allah ya fada ta Agape cewa wannan shine lokacinmu. Na gode Agape.” Gwamnan ya kara da cewa.
Gwamnan ya yabawa shugabannin Cocin bisa bin umarnin gwamnati kan sanya na’urar CCTV a wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a.
Akeredolu ya godewa Allah da ya sanya aka kama wadanda suka kai hari cocin St Francis Catholic Owo, yana mai cewa addu’a ce ta amsu.
Daga nan ya bukaci jama’a da daukacin al’ummar jihar da su kasance masu lura da tsaro a kodayaushe kuma su kasance cikin shiri.
“Don Allah mu kasance a faɗake kuma mu kasance masu lura da tsaro. Tsaronmu yana hannunmu, dole ne mu kasance a faɗake. Allah zai cigaba da kare mu baki daya.
“Duk abin da gwamnati ta ce ku yi, don Allah ku bi. Ku sa jami’an tsaro a ƙofofinku, ku sa kyamarorinku na CCTV ku duba duk sabbin fuskoki kafin ku ba su izinin shiga cocin ku.”
Gwamnan, wanda ya gargadi wadanda ke aiki a matsayin masu ba da labari ga masu garkuwa da mutane a jihar, ya jaddada cewa duk wani, sansani ko kauyen da ke taimakawa masu garkuwa da mutane a jihar za a shafe su.
Babban mai kula da cocin Agape International Church, Bishop Felix Adejumo ya bayyana Gwamna Akeredolu a matsayin muryar yankin Kudu maso yamma wanda ya yi matukar kokari wajen kare martabar jihar Ondo da ma daukacin yankin Kudu maso Yamma.
(NAN)