Shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, ya zama wajibi jam’iyar ta lashe kafatanin zabukan da za’a gudanar a babban zaben shekarar 2023.
Adamu ya ce, wajibi ne APC ta samu gagarumin nasara a zaben shugaban kasa, Yan majalissu, da zabukan gwamnonin jihohi a 2023.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Laraba a babban birnin tarayya Abuja Adamu ya jaddada cewa, Da yuwuwar Jam’iyar APC ba zata lamunci kashi 25 cikin dari kacal ba.
“Duk zabukan kasa, ‘yan majalisar wakilai, dattijai, gwamna, musammanma zaben shugaban kasa, ba za mu gamsu da kashi 25 na kuri’un da aka kada ba.
APC tace zata samo Ƙuri’un Masu Buƙata ta Musamman Miliyan 25 ga Tinubu a 2023
“Babu wata hanya bayan hakan, I dan za mu yi nasara, ya zama wajibi muyi kokarin lashe zaben a kowace jiha” inji Adamu.
.
Kazalika Shugaban jam’iyar APCn na kasa ya bukaci yayan jam’iyar da su tabbatar sun dinke barakar dake tsakanin su, domin samun nasarar Jam’iyar a babban zaben 2023.
A wnai labarin kuma na daban.
Da Ɗuminsa: APC ta tabbatar da Lalong a matsayin DG na yakin neman zaben Tinubu
A ranar Alhamis din da ta gabata ne jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da Gwamnan Jihar Filato kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong a matsayin Babban Darakta na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa.
Shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan ga Manema Labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
Ya ce, “Mun zo nan ne domin ganin shugaban kasa da yi masa bayani da kuma samun amincewarsa kan tsare-tsaren da muke yi dangane da yaƙin neman zabe.
“Kuma da zarar mun sami yardarsa, zamu yi bayani. Muna tare da Shugaban kasa da kuma daidaikun mutanen da za su taka rawa daban-daban a yakin neman zabe.
“DG na kamfen yana zaune a dama na a nan. Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato.
“Mai magana da yawun shine Festus Keyamo. Mataimakiyar kakakin ita ce Hannatu Musawa Wannan shi ne abin da muka zo don tattaunawa da shugaban kasa.”
Adamu ya bayyana cewa zaben Lalong ya ta’allaka ne kan yadda ya iya yin ayyukan da ake bukata domin tabbatar da nasarar tikitin Tinubu-Shettima a zaben shugaban kasa na badi.
“Yana da ikon yin hakan. Shugabancin jam’iyyar ya ga cewa yana iya tafiyar da harkokin kamfen din,” in ji shi