Kotu ta tura Dan gidan Mai baiwa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Shawara na musamman akan bunkasa saka hannun jari Aminu Hayatu Tafida, da wasu mutum biyu zuwa gidan yari na tsawon Shekaru hudu da watanni shida.
Wadanda aka daure tare da Aminu Hayatu, sun hada da Umar Abubakar da Masa’ud Abubakar Gidado, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita.
An dai basu zabin biyan tara na Naira dubu dari 400,000 ciki harda biyan diyya, sakamakon zargin su da yada bidiyon badala na tsawon dakika 18 a wata kara da aka dade ana d’agewa.
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC ta kama Mutane 30 da take zargin Masu Damfara ta yanar gizo ne a Kwara
Dayake yanke hukunci a ranar Talata Babban Majistare Shu’aibu Ahmad na Kotun Majistare dake zaman ta a Sokoto yace, lauyan dake shigar da karar ya kawo dukkanin hujjojin da ake bukata, a dalilin haka ya sanya dukkanin su aka yanke masu hukunci, akan laifin da suka aikata.
A lokacin daya karanto sashi na 209 na kundin tsarin gudanar da Shari’a na Sokoto na Shekarar 2019, Shu’aibu ya baiwa lauyan dake kare wadanda ake karar damar gudanar da wasu hujjoji kafin zartar da hukunci.
A dalilin haka, lauyan dake kare wadanda ake karar, yace basu da niyyar kirawo wani shaida akan Shari’ar, inda suka bukaci a gudanar da hukuncin cikin adalci, kasancewar dukkanin wadanda suka aikata laifin matasa ne da suke da shekaru masu yawa anan gaba, a saboda haka, akwai bukatar a basu zabin su biya tara.
“Muna kira ga wannan kotu mai adalci data yi tausayi a hukuncin ta. Muna kuma kira ga wannan kotun data bada wani zabi,inji lauyoyin
A zartar da hukuncin, Mai kula da gudanar da Shari’ar Shu’aibu Ahmad, yace ya lura dacewa, dukkanin wadanda suka aikata laifin shine na farko da suka taba aikatawa, a saboda haka za’a tausaya masu a hukuncin tare da basu kayyadajjen shekaru.
Shu’aibu yace dabi’ar yada bidiyon batsa ya sabawa sashe na 171, don haka wadanda ake karar zasu biya Naira dubu dari 200,000, Wanda zai kaiga yanke masu hukunci na tsawon shekaru biyu.
Sauran laifukan da suka hada da Saida littattafan batsala zasu biya Naira dubu Hamsin-Hamsin da diyyar Naira dubu dari 100,000.
Da suke magantawa akan hukuncin, dukkanin masu shigar da karar ASP Simon Sule da masu karar, duk sun nuna gamsuwa da hukunci, suna masu bayyana cewa zai zama izna ga wadan su.
Comments 1