Yadda Ƴan Sanda Suka Ceto Masu Garkuwa Da Mutane Daga Hannun Fusatattun Matasa
Rundunar Ƴan sandan jihar Delta ta ce ta ceto wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne daga hannun wasu fusatattun mutane.
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta karkashin jagorancin CP Ari Muhammed Ali ta tabbatar da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sandan DSP Bright Edafe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sai Mun Binciko Duk Mai Hannu A Kisan Sheikh Aisami— Gwamna Buni
Ya ce, “A wurin bincike, an gano cewa ana zarginsu da yin garkuwa da mutane.”
A cewar DSP Edafe, “wata mata kuma ta zargi mutane da yin garkuwa da Ɗanta mai shekaru 17 a safiyar ranar.
“Wadanda ake zargin, Oti Shevire mai shekaru 32 da haihuwa da Amos (wanda ba a san sunan sa ba), bayan an yi musu tambayoyi, sun amsa laifin da suka aikata, sannan sun kai ƴan sanda zuwa maɓoyar su, inda aka ceto wani, kuma a halin yanzu yana samun kulawa. Waɗanda ake zargin suna tsare kuma ana ci gaba da gudanar da bincike akan su.