Wani Udam Samuel Aswear daga Jihar Binuwai ya koka akan yadda ‘yan zaman makoki su ka sace kujeru bakwai wadanda ya yi hayarsu don birniyar mahaifiyarsa a ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamban 2022, LIB ta ruwaito.
KU KARANTA: Kyakkyawa mai mazaunai da albarkar ƙirji kuma ƴar masu kuɗi nake so, Matashi na neman aure
Kamar yadda yace:
“Ka je biriniyar mahaifiyata kuma an sace kujeru 7 cikin wadanda aka aro, hakan yasa sai da na biya N25,200 (ko wacce kujera 3,600)” kamar yadda ya rubuta ranar Litinin.
“Ina kauye tun jiya akan wannan lamarin kuma ban samu mafita ba. Sai da na cika sharuddan aron kujerun sannan aka ba ni.”
Hotunan kashe kalar da wani matashi yayi, har da lulluɓe motarsa da irin kayansa
Idan aka zo batun daukar wanka, akwai wadanda ba za su taba yarda a bar su a baya ba, Legit.ng ta ruwaito.
Nan da nan mutane da dama su ka yi caa su na tsokaci iri-iri tare da yada bidiyon a TikTok, bayan ganin yadda shigarsa ta dauki hankula.
A cikin bidiyo an ga yadda ya sanya riga da wan don atampa tare da wani matsattsen wando wanda daga gani tela ne yayi.