A gasar rukuni-rukuni ta ƙaaar Netherlands ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ajax ta ragargaji ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta VVV VENLO daci 13 da nema awasan da suka fafata a daren jiya. Wannan ƙwallaye 13 da Ajax ta zura sun shiga kundin tarihi a gasar ta ƙasar Holland.
A kakar wasa ta bana dai anayin yayin yin wannan wanakan jegon na zura ƙwallaye da yawa duba da yadda aka kwararawa Manchester City ƙwallaye 5 har gida a gasar ajin Firimiyar Ingila. Haka zalika itama Manchester United Tottenham ta zabhamata ƙwallaye 6 har gida. Idan ba a manta ba itama zakarar gasar ta Premier wato Liverpool itama Aston Villa ta wanke ta da ƙwallaye 7 – 2.
Wannan kakar wasan ta bana dai ana ganin tabbas za ayi ruwan ƙwallaye da yawa inda wasannin suka nuna akan mayar da gidan wata ƙungiyar ƙwallon ƙafan kamar ba gidanta ba inda akan yimusu wanka da ƙwalalye masu yawa.
Ajax dai itace ta zamo ƙungiyar datafi jefa ƙwallaye da yawa a wasa guda a kakar wasa ta bana ganin yadda ta zuwa ƙwallaye guda 13 a gasar ta rukuni-rukuni da ake gudanarwa a ƙasar ta Netherlands.