Wani magidanci ɗan ƙasar South Afrika mai suna, Phasha Manapyane, ya bayyana wani labari domin nuna muhimmincin mutane su tashi su nemi ilmi.
A cewar Phasha, matarsa wacce bata yi karatu ba ta siyar da gidansu ga wani ɗan damfara ba tare da sanin cewa damfararta akayi ba. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Shugabannin wasu kasashe biyu sun taya Tinubu murnar cin zabe
Yayi ikirarin cewa ɗan damfarar ya zo gidan su ne inda yayi basajar zama mai kawo saƙon Pizza, amma abin mamakin shine basu ce a kawo musu Pizza ba.
Lokacin da aka ba matar Phasha takarda ta sanya hannu, sai kawai ta sanya ita a tunaninta ta sanya ne domin nuna cewa ta karɓi saƙon.
Amma abinda bata sani ba shine, ta sanya hannu ne kann yarjejeniyar cinikayya, wacce bata sani ba saboda bata yi karatu ba.
Magidancin ya bayyana wannan labarin takaicin ne a manhajar Facebook, bayan wani mutum mai suna Alu Ndou yayi tambayar;
“Shin karatu yana da muhimmanci wajen zaɓen abokin rayuwa? Kawo amsar ka da hujjoji.”
Phasha sai ya rubuta:
“Wani mutum ya kawo mana Pizza wacce bamu ce a kawo ba kuma muna buƙatar mu sanya hannu. Ni bana gida lokacin. Matata sai ta sanya hannu, hakan shine silar siyar da gidan mu.”
Magidanci Ya Arce Bayan Matarsa Ta Kara Haiho Masa Diya Mace
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya gudu ya bar matarsa a asibiti bayan ta kara haiho masa diya mace.
Wani magidanci ɗan Najeriya ya tafi ya bar matar sa a asibiti saboda ta ƙara haiho masa jaririya yayin da shi kuma yake son jariri namiji.
Wata ma’aikaciyar jinya da unguwar zoma a jihar Legas, mai suna Kaykay, itace ta bayyana hakan a manjahar TikTok a ranar Juma’a 31 ga watan Maris 2023.