Hukumar dake shirya gasar share fage ta yammacin nahiyar Afrika ta fitar da ranakun da za a fafata wasannin share fage na ‘yan ƙasa da shekaru 17 da kuma ‘yan ƙasa da shekaru 20 na ƙasashen Afrika ta yamma, an fitar da rukunan A dana B a dukkannin ajujuwan guda biyu wato ‘yan shekara 17 da ‘yan shekara 20.
Ga yadda aka fitar da rukunan share fagen na ‘yan ƙasa da shekaru 20:
Rukunin A an fitar da ƙasashen Burkina Faso da Bénin da Togo da kuma ƙasar Niger.
A rukunin B kuwa an fitar da jerin ƙasashe kamar su Nigéria da Côte d’Ivoire da kuma Ghana
Za a buga wasannin share fagen daga ranar 18 ga wagan Nuwamba zuwa ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 2020.
Shikuwa rukunan ‘yan ƙasa da shekaru 17 an fitar da rukunin A da B kamar yadda aka fitar dana ‘yan ƙasa da shekaru 20.
Ga yadda aka fitar da rukunan:
Rukunin A an fitar da ƙasashe kamar su Togo da Bénin da Niger da kuma Burkina Faso.
Haka zalika a rukunin B akwai ƙasashe irinsu Ghana da Nigeria da kuma Côte d’Ivoire.
Za a fara fafata wasannin share fagen a ranar 5 zuwa 20 ga watan Disamba na shekarar 2020.
Dukkanin ƙasashen da sukayi gagarumar nasara to sune zasu wakilci Afrika ta yamma a wasannin gasar cin kofin nahiyar Afrika ta ‘yan ƙasa da shekaru 17 da kuma ‘yan ƙasa da shekaru 20 daza a fafata a nan gaba kenan wato a sabuwar shekara mai kamawa ta 2021.